<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><author>Monk, William Henry (1823-1889), Lyte, Henry F. (1793-1847)</author>
<lyrics>[V1]
 1) Ni Allahnka ne, Ubangijinka,
 Ba za ka shiga bautar wani ba.
 Gare ni za ka dogara kaɗai,
 Ni ma zan kiyaye ka zuwa rai

[V2]
 2) Ba za ka yi wa kanka sura ba,
 Sura ta sama ko ta duniya.
 Ba za ka yi musu sujada ba,
 Ni, Ubangiji, za ka bauta wa.

[V3]
 3) Ba za ka ƃāta sunan Allah ba,
 Ba za ka gama shi da ƙarya ba,
 Amma a cikin duk bukatarka
 Yi roƙo fa tare da godiya.

[V4]
 4) Ka tuna da rana mai tsarki,
 Cikinta za ka daina aikinka.
 Sai dai ka tuna da maganata,
 Ka nemi ceton ƴanuwanka kuwa.

[V5]
 5) Uba da uwa za ka girmama,
 Maganarsu ba za ka raina ba.
 Biyayya za ka yi gare su kuwa,
 Ni ma zan sa maka albarkata.

[V6]
 6) Kisa ba za ka yi shi ba lalle.
 Ba za ka ɗauko fansa ba daɗai.
 Ba za ka ƙi wanda ya ƙi ka ba,
 Ƙaunarsa za ka yi har abada.

[V7]
 7) Zina da fasikanci za ka ƙi,
 Kada ka ko yi tunaninsu fa.
 Sai ka yi zamanka da tsabtar rai,
 Kiyaye aurenka da tsarkin rai.

[V8]
 8) Kada ka yi sata ko yaudara.
 Ba za ka ƙwace kayan kowa ba,
 Amma ka yi aiki da hannunka,
 Ka riƙa taimakon matsiyata.

[V9]
 9) Kada ka yi wa kowa shaidar zur.
 Shaiɗan ne uban masu ƙarya,
 Tsegumi da makirci nasa ne,
 Dukansu dole za ka ƙi sosai.

[V10]
 10) Kada ka yi ƙyashin kayan mutum.
 Kada ka nemi mata tasa kuwa.
 Yi aikin ƙauna da makusanta,
 Yadda kai ka ke so a yi maka.</lyrics>
<title>Ni Allahnka Ne, Ubangijinka LW243</title>
<hymn_number>243</hymn_number>
</song>